A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a cikin wata sanarwa da aka fitar, Babbar Hedkwatar Sojojin Iran ta bayyana cewa, duk da sanarwar da wasu kasashen yankin suka bayar a hukumance cewa ba za su bari sojojin Amurka su yi amfani da yankunansu, sararin samaniyarsu ko ruwansu wajen kai hari kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba, har yanzu ana zargin sojojin Amurka da amfani da yankunan, sararin samaniya da kuma wuraren da ke karkashin ikon wasu daga cikin kasashen wajen kai hare-hare kan Iran da wasu cibiyoyin soji.
Sanarwar ta kara da cewa, kamar yadda sojojin Iran suka nuna a fagen daga a baya, suna mutunta ikon mallakar kasashen makwabta na kasa, amma ba za su taba lamuntar wani nau'in mamaya ko kai hari daga yankinsu ba.
Ta ce duk wani sabon hari da aka kaddamar daga wata kasa za a mayar masa da martani mai matukar nauyi, tana mai nuni da cewa an riga an tabbatar da hakan a daren da ya gabata ta hanyar ayyukan jaruman dakarun Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) da kuma Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Hedkwatar sojojin Iran ta jaddada cewa, sojojin Amurka ba su da wata mafita face ficewa daga yankin, tare da gargadin wadanda ke saukaka wa Amurka kai hari kan Iran cewa, dakarun sojin Iran, ciki har da IRGC da Sojojin Jamhuriyar Musulunci, za su hada karfi wuri guda wajen kai hari mai tsauri kan duk inda aka fara kai musu farmaki.
Sanarwar ta kuma yi gargadi ga wadanda ke barazana ga Iran, inda ta ce al'ummar Iran da dakarunta sun sha fuskantar irin wadannan gwaje-gwaje a baya, kuma ba za a amince da sake gwada karfin ikonsu da juriyarsu ba.
Babbar Hedkwatar Sojojin Iran da Babban Sansanin Khatamul Anbiya (A.S) sun jaddada cewa duk wani hari da ya samo asali daga wata kasa zai fuskanci martani mai tsanani.
Ra'ayinka